SiyasaJamus
ECOWAS ta kakaba wa Mali takunkuman tattalin arziki
January 10, 2022Talla
Kasashen sun ce za su tsananta wa Malin ne ta fuskatar rufe iyakoki da ma haramta cinikayya a tsakaninsu.
Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin na Afirka ECOWAS ce ta yanke wannan shawara a taronta na koli da aka yi a Ghana.
Za ma a yanke duk wani abu mai nasaba da tallafin kudade ga Malin, da ma rufe asusunta a babban bankin kasashen ECOWAS.
Jagororin gwamnatin Mali a Bamako, sun ce zabe a Mali sai bayan shekaru hudu nan gaba, sabanin watan Fabrairu da suka amince da fari.