1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta yarda da ficewar Mali da Nijar da Burkina

Ubale Musa Abdoulaye Mamane
December 15, 2024

A babban taron kolin shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS/CEDEAO, kungiyar ta amince da ficewar kawancen AES da suka hada da Mali da Burkina Faso da Nijar

Shugabanin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS/CEDEAO
Shugabanin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS/CEDEAO Hoto: Ubale Musa/DW

Bayan shafe tsawon lokaci ana kai kawo, hukumar gudanarwa ta ECOWAS/CEDEAO ta amince da bukatar kasashen kawancen Sahel na ficewa daga kungiyar kasashen raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirka. A kashen taron wuni daya da shugabannin kasashen kungiyar suka gudanar a Abuja na Najeriya, jagororin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO din sun nuna amincewa da bukatar da kasashen uku suka mika musu na janyewa daga kungiyar daga 29 ga watan Janairu na 2025 da ke tafe.

Karin bayani: Taron ministocin tsaron ECOWAS a Abuja

Kungiyar ta kara wa kasashen na Mali da Nijar da Burkina Faso karin wa'adin watanni shida, har zuwa 29 ga watan Yuli na 2025 da nufin ganin ko za ta sake mayar da kasashen guda uku zuwa ga kungiyar. Shugabannin kasashen sun kuma amince da nada shugabannin Togo da Senegal da su cigaba da tattauna wa da kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso har zuwa cikar wa'adin da nufin ba su hakuri ko sun aminta da sauya matsayi.

Taron kasashe mambobin kungiyar ECWAS/CEDEAO a Abuja na NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

Karin bayani: Hanyar da sojin ECOWAS za su bi wajen inganta tsaro

Duk da dusashewar taron kan yankin Sahel, kasashen sun yi farin ciki da nasarar zaben Ghana, wanda ke zaman wata fitilar da ke haskaka zuciyar da dama mahalarta taron na Abuja, inda shugaba Bola Tinubu da ke jagorantar ECOWAS din bai boye farin cikin da kasashen yankin ke yi ba bisa rawar da 'yan siyasar Ghana suka taka ba.Batun tsaro da karuwar barazanar ayyukan ta'addanci na tayar da hankalin kungiyar ECOWAS/CEDEAO inda suka yi wa batun nazarin kwa-kwaf, sai dai kuma taron ya yi la'akari da cewa rigingimun makiyaya da manoma sun ragu a kasashen yankin, kana kuma ayyukan barayin teku ya inganta ta yadda ba a samu wata sata a teku ba a daukacin shekarar bana. Sai dai kuma tattali na arzikin kasashen yankin ya karu da kaso 3.8 a shekarar da ke shirin karewa, wani abun da ke nuna alamu na ci gaban al’ummar yankin.