1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An dauki matakan ladabtar da sabbin mahukuntan kasar Guinea

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
September 17, 2021

Kungiyar ECOWAS ta kakaba wasu jerin takunkumai kan jagororin da suka kifar da gwamnatin farar hula a kasar Guinea-Conakry. Shugabannin kasashen kungiyar sun dauki matakin toshe kudaden sojojin da iyalansu.

Guinea Junta
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Daukacin shugabannin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da suka halarci wani taro ranar Alhamis a birnin Accra na kasar Ghana, sun cimma matsaya guda na kakaba jerin takunkumai ga sojan da suka kifar da gwamnatin kasar Guinea karkashin jagorancin Kanal Mamady Doumbouya a farkon wannan wata.

Wasu daga cikin matakan ladabtarwar da kungiyar ta dauka masu tsauri irinsu na farko a tarihinta ga wata kasar da aka yi juyin mulki, sun hada da hana sojan da suka yi juyin mulkin duk wasu tafiye-tafiye a cikin kasashen kungiyar baya ga kakaba takunkumi ga kudaden da suka mallaka.

To amma babban abin da ya fi daukar hankali shi ne na ganin an dawo da kasar kan tafarkin dimukuradiyya, wanda a sanarwar bayan taronsu shugabannin suka ce dole ne sojan su mika mulki a hannun wata gwamnatin nan da watanni shidda.

Karin bayani: Kungiyar AU ta dakatar da Guinea Conakry

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS, Jean-Claude Kassi Brou ya nunar da cewa "Dole ne a takaita wa'adin mulkin sojan kuma shugabannin kungiyar sun ce bai dace ta wuce watanni shidda ba, sun matsa kan wannan wa'adin saboda a cewarsu hakan ne kawai ka iya ba wa kasar dawowa a kan turbar dimukuradiyya a Guinea."

Tawagar kungiyar ECOWAS da ta tattauna da jagororin sojin Guinea a birnin Conakry a farkon watan SatumbaHoto: Präsidentschaft Guineas

Kungiyar ta bayyana cewa matakin da ta dauka ya shafi mutane da suka yi juyin mulkin wanda hakan ya saba wa tsarin dokokinta.

Kana kuma shugaban hukumar zartarwar kungiyar cewa ya yi matakin na a matsayin wata manuniya da ishara kan duk wani wanda ke da yunkuri ko ma marmarin kifar da gwamnati a bainar kasashen ta hanyar amfani da karfin soja.

"Daukar wannan matakin na nufin ne da cewa karara muna bukatar ladabtar da membobin hukumar ta CNDR da suka karbe mulki da tsinin bindiga, domin kuma ya kasance wata ishara ga wadanda suke da duk wata irin wannan manufar ta karbe iko ta hanyar da ta sabawa tsarin mulki da dimukuradiyya."

Karin bayani: Guinea ta zama saniyar ware a ECOWAS

Kungiyar ta kuma bukaci da a saki hambararren shugaban kasar Alpha Conde da ke hannun sojan da suka kifar da gwamnatinsa tun a farkon wannan wata kamar yadda ta bukata tun daga farko.

Sai dai ana gudanar da wannan matakin ne a daidai lokacin da rundunar sojan a Guniea-Conakry take ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarori na al'ummar kasar da zummar duba hanyoyin tafiyar da gwamnatin ta wucin gadi wacce shugaban sojan ya ce al'ummar kasar ne kadai ke da hurumin shatawa.

Shugaban gwamnatin mulkin soji Kanal Mamady Doumbouya jim kadan baya kifar da gwamnatin farar hulaHoto: Radio Television Guineenne via AP/picture alliance

Sai dai Kanal Mamady Doumbouya ya bukaci taimakon kasa da kasa don ganin ya kammala mulkin wucin gadi a yayin tattaunawarsa da wakilan kasashen ketare.

"Muna da bukatarku kusa da mu don agaza mana kawo karshen wannan tsarin ba tare da katsalandan ba ko matsin lamba, ta hanyar amfani da hanyoyin da muka shata na gaskiya. Muna kuma fatan ganin kun dafa mana ta hanyar kauna da zumunci da huldar da muke da ita da ku, don rarraba ababe na gaskiya da za su ba mu damar farfado da kimar kasarmu."

Yanzu haka ana dakon ra'ayin da sabbin hukumomin kasar ta Guinea-Conakry za su bayar game da sabon matakin na ECOWAS. Kana kuma ana dakon isar shugaban Ghana a kasar don tattaunawa da hukumomin mulkin sojan game da batutuwan da ECOWAS din ta tsayar da ma wasu sabbin hanyoyi na shirya mika mulki ga farar hula.