1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta tsawaita wa'adin zaman sojojinta a Gambiya

Gazali Abdou Tasawa MNA
June 5, 2017

Kungiyar ECOWAS ta tsawaita wa'adin zaman sojojin rundunarta ta Micega a Gambiya da shekara daya.

Gambia Soldaten der ECOWAS Truppen aus Senegal bei Denton check point in Banjul
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO ta tsawaita wa'adin zaman rundunar sojojinta a Gambiya da shekara daya. Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar karshen zaman taron kolinta da ta gudanar a birnin Monroviya na kasar Laberiya a ranar Lahadi inda ta ce ta dauki matakin ne ta la'akari da raunin tsaron da kasar take da shi har yanzu. 

Kungiyar ta ECOWAS ta kuma ce sojojin rundunar ta Micega za su taimaka wajen horas da sojojin kasar Gambiyar da ma sake fasalin rundunar sojin kasar baki daya. 

A watan Janerun da ya gabata, bayan da Shugaba Yahya Jammeh ya fice daga kasar a bisa matsin lambar kungiyar ta ECOWAS, aka kafa rundunar ta Micega wacce ke kunshe da sojoji akalla 500 akasarinsu daga Senegal da Najeriya da Ghana domin maido da zaman lafiya da kuma kare lafiyar sabon shugaban kasar Adama Barrow. 

Sai dai yanzu haka wani sashe na al'ummar kasar na yawan tayar dar tarzoma domin nuna adawa da zaman rundunar musamman a mahaifar tsohon Shugaba Yahya Jammeh.