ECOWAS ta yi tir da juyin mulkin soji a Mali
March 22, 2012A martanin sun na farko game da juyin mulkin da ya hamɓarar da gwamantin Amadou Toumani Toure a ƙasar Mali, tarrayar Najeriya da kuma ƙungiyar gamayyar tattalin arzikin ƙasashen yankin yammacin Afika ta ECOWAS sun ce ba za su lamunci matakin sojan na kawo ƙarshen mulkin demokraɗiyyar ƙasar ta Mali ba.
An dai kai ga bugar ƙirji da kiran adabo da duk wani ƙoƙari na juyin mulki, to sai dai kuma ana shirin shan mamaki a yankin yammacin Afirka na ECOWAS da ya wayi gari da wani juyin mulkin sojan da ke zaman ba zata da kuma ya ta da hankula a ciki da wajen yankin.
A Abuja dai ana ci gaba da kartar ƙasar ba'a isa ba kama daga ita kanta hedkwatar hukumar gudanarwar yankin ta ECOWAS da ta ce ba za ta karɓi duk wata gwamantin da ta ƙwaci mulki da ƙarfin hatsi ba, ya zuwa fadar gwamantin Najeriyar da ita ma ta fito ta yi Allah wadai da matakin da shugabanta Goodluck Jonathan ya kira gagarumin ci baya ga demokraɗiyya da mulki na gari a tsakanin ƙasashen.
Rikicin tawayen arewacin Mali ya janyo juyin mulki
Juyin mulkin da ya zo dai dai lokacin da kasar ta Mali ke ƙoƙarin kawo ƙarshen wani tawayen Abzinawa dakea zaman wani babban ƙalubale ga shugabanin ƙasashen yankin 15 da suka share tsawon shekaru kusan biyun da suka gabata suna neman mafita ga jerin rigingimun da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.
Tuni dai wata tawagar kungiyar ta ECOWAS ta bar Abuja zuwa Bamako domin nazarin halin da ake ciki da kuma sanin mataki na gaba da ya kamaci yayan kungiyar dauka da nufin sake dawo da demokradiyya da mulki na gari
Tuni dai manyan kasashen duniya suka bi sahu wajen tofin ala tsine dama daukar matakin dakatar da dul wani hadin kai da taimako a tsakanin su da kasar da ta dade tana dogaro da agajin turawan yamma domin rayuwa da cigaban alummar ta
Ƙungiyoyin farar hular ƙasashen yankin sun nemi bijirewa sojojin na mali a cewar Dr jibrin Ibrahim dake zaman shugaban kungiyaoyin farar hular kasashen yankin na ECOWAS.
To sai dai kuma ko ya take shirin wanyewa a tsakanin talakawan kasar ta mali da kuma sabbabin mammalakan nasu dai juyin mulkin har ila yau na kara fitowa fili da irin girman barazanar da tasirin rikicin kasar Libya mai makwabtaka da kasashen na ECOWAS ke cigaba da haifarwa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummarsa miliyan 250.
Tasiri Al-Qaida na ƙaruwa a Afirka ta Yamma
Ko bayan juyin mulkin da ake ta'allakawa da galabar da Abzinawan da suka samo makamai da ma ƙwarewar yaki a Libiyan yanzu haka kuma ke riƙe da kusan rabin kasar ta Mali ke samu a gwagwarmayar neman rabon kasar,
Kasashen yankin har ila yau na kuma fuskantar matsalar karuwa da tasirin kungiyar Al-Qaida da kuma yan uwansu na boko haram a tarrayar nigeriar dake zaman mafi girma a yankin.
An dai share tsawon makon jiya ana shelar neman agajin makamai da kuɗi da nufin taimakawa kasar murƙushe yan tawayen dake rike da fiye da rabin ƙasar ya zuwa yanzu.
Abun jira a gani dai na zaman makomar ƙasar da a baya ake yiwa kallon na kan gaba ga ƙoƙarin tabbatar da demokradiya da mulki na gari a ɗaukacin yankin na ECOWAS.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal