1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Juye-juyen mulki a yammacin Afirka sun mamaye taron ECOWAS

Abdoulaye Mamane Amadou
March 25, 2022

A birnin Accra na kasar Ghana, shugabannin kasashe membobin kungiyar ECOWAS na halartar taron koli kan batun juye-juyen mulkin da aka yi a wasu kasashe uku na yammacin Afirka.

Nigeria | taron ECOWAS
Hoto: Präsidentschaft von Niger

Za a gudanar da taron a birnin Accara na kasar Ghana kuma ana sa ran shugabannin kasashen su kara daukar muhimman matakai ga sojojin da suka aiwatar da juyin mulki a kasashen Burkina Faso da Guinea Conakry, bayan dakatar da su daga jerin membobin kungiyar. Kana ana hasashen kungiyar ta shata wa sojojin da suka yi juyin mulkin wa'adin sake mika mulki a hannun wata gwamnatin farar hula.

Sai dai ana ganin batun jadawalin shirya zabe a Mali, zai kasance kan gaba daga cikin muhimman batutuwan da taron na ECOWAS zai mayar da hankali, musamman ma bayan da kungiyar ta kasa cimma matsaya da gwamnatin rikon kwarya a karkashin jagorancin Kanar Assimi Goïta kan batun wa'adin shirya zabe.