1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Taron ministocin tsaron ECOWAS a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 8, 2024

Ministocin tsaro na kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO karkashin Kwamitin Tsaro da Sulhuntawa, na taro a Abuja.

Najeriya | Abuja  | ECOWAS | CEDEAO | AU
Taron inistocin tsaron kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a Abujan NajeriyaHoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Ministocin tsaro na kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen  Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO karkashin Kwamitin Tsaro da Sulhuntawar, sun fara wannan taron a Abuja fadar gwamnatin Najeriya ne da nufin tattaunawa kan sanarwar daukar matakin ficewa daga cikin kungiyar da shugabannin gwamnatocin mulkin soja na kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma  Burkina Faso suka yi.

Karin Bayani: Martanin kasashe kan ficewar wasu daga ECOWAS

Matakin wadannan kasashe uku dai, ya haifara da damuwa a kan sakamakon da zai haifar ga kasashen da ma kungiyar kanta. Baya ga batun ficewar kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Fason ministocin tsaron kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO, za kuma su tattauna batun dakatara da gudanar da zaben da shugaban Senegal Macky Sall ya yi a kasar da ya kara haifar da barazana ga tsarin dimukurdiyya da ke kara shiga mawuyacin hali a yankin.

Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré Burkina FasoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Shugaban Hukumar ECOWAS din Omar Alieu Touray ya ce, suna fuskantara kalubale da ke son hadin kai. Bisa ga abubuwan da suke faruwa da matakin farko da kungiyar ta dauka a kan kasashen guda uku da suka sanar da aniyasru ta ficewa daga cikinta da Kwamitin Tsaro da Sulhuntawa ke yi, akwai alamun kungiyar ta fara sassautowa domin bin hanyar lalama wajen sasantawa. Tun da farko dai wakilin kungiyar Tarayyar Afirka AU a wajen taron kana kwamishina tsaro da harkokin siyasa 

Karin Bayani:Mali da Burkina Faso da Niger za su karfafa hulda

Ambasada Bankole Adeoye ya bayyana damuwar kungiyar ne, kan halin da ake ciki a Senegal bayan dakatara da gudanar da zabe da shugaban kasar ya yi. Ya bayyana cewa kungiyar ta AU, na goyon bayan kungiyar ECOWAS a wannan mawuyacin hali da ake ciki. Ficewar kasashen uku na Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso dai, ya sanya fusknatar barazana ta tsaro da zamantakewa da kuma ta tattalin arziki. Amfani da kalamai na lalama da lallashi dai, sabuwar dabara ce da kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ke dauka a kan wadannan matsaloli da ke barazana ga kasashen da ke son ficewa da ma kungiyar kanta.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani