1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS: Tunkarar rashin tsaro a yammacin Afrika

January 30, 2026

A wani abun da ke zaman jan aiki ga kokairin tunkarar rashin tsaro a yammacin Africa, kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta ce janyewar kasashen Sahel guda Uku na dagula lamura a kokarin tunkarar yakin

Shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS
Shugabannin kungiyar kasashen ECOWASHoto: Ubale Musa/DW

ECOWAS din dai ta ce rashin isashen hadin kai na kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso na kawo cikas ga kokarin kai karshen annobar ta’addanci.

Janyewar Nijar a rundunar tafkin Chadi da rushewar yar uwarta ta G5 Sahel dai ya zamo kafa ta masu ta'addar na cin karensu babu babbaka

An dai share shekaru guda biyu ana kallon kallo, to sai dai daga dukkan alamu ana ganin tasirin rikici na siyasa da ya raba kai tsakanin kasashen da ke yammacin Afrika.

Duk da cewar a cikin kawancen Sahel an gintse, nan cikin kasashen ECOWAS tuni aka fara korafi na dagula lamura cikin batun rashin tsaro da ta'addanci, sakamakon janyewar kasashen yankin guda Uku.

Karin Bayani:John Mahama na yunkurin shiga tsakanin ECOWAS da kasashen Sahel

Taron kolin shugabannin kungiyar kasashen ECOWASHoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

Shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS Alioun Tourey yace kasashen yankin basa samun cikakken hadin kan kasashen kungiyar kawancen Sahel din cikin batun rashin tsaron da ke a yankin Sahel yanzu.

Duk da ragowar harin da ke faruwa a yankin yanzu Tourey ya ce sauyin salo da ma makamai na masu ta'addar na kara yawan zubar jini da ma rasa rayukan al’ummar ECOWAS din.

An dai share shekaru biyu ana zaman yan marina, amma kuma har yanzu an gaza kirgar riba walau a bangaren ECOWAS ko na kawancen cikin batun rashin tsaron mai tasiri.

Wani rahoto na kasa da kasa bisa- batun rashin tsaron a shekarar da ta shude dai, alal misali , ya saka kawayen Sahel akan gaba cikin kasashe biyar na duniya mafi ji a jiki, kafin tarayyar Najeriya ta hau mataki na shida

Karin Bayani:Bukatar sauyi a kungiyar ECOWAS ko CEDEAO

Taron kolin shugabannin kungiyar kasashen ECOWASHoto: Ubale Musa/DW

A watan Maris na shekara ta 2025 ne dai Nijer ta janye daga rundunar gamin gambizar tafkin chadi da ke jagorantar annobar Boko Haram kafin rushewar kungiyar G5 Sahel.

Duk da sakamakon juyin mulkin da ya kai ga farraka cikin kasashen yankin ko a wannan makon an ga wani harin a filin jirgin saman Yamai, da kila aiken sakon girman rashin tsaron da ke cikin yankin yanzu.

Koma wane tasiri ake shirin gani cikin kasashen yankin dai, kyale siyasar hawa na kan gaba akan tsaro da makomar al’umma, na iya jefa daukacin mutanen yankin a cikin hatsarin da ke da girman gaske.

Rashin tsaron da ke kasashen yankin dai na tasiri ga tattalin arzikin al’ummar da ke da arziki maras adadi amma kuma ke zama kan gaba cikin talauci a duniiya baki daya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW