ECOWAS za ta gudanar da taro kan Burkina
November 5, 2014![Westafrikanische Präsidenten fordern zivile Regierung in Burkina Faso 05.11.2014](https://static.dw.com/image/18043767_800.webp)
Talla
Shugaban ƙasar Ghana john Mahama Dramani kana shugaban Ƙungiyar gamayya tattalin arziki ta ƙasashen yankin yammacin Afirka wato ECOWAS.
Ya ce gwamnatin riƙon ƙwarya da za a girka a nan gaba a Burkina Faso za ta ɗauki tsawon wa'adin shekara guda,sannan ya ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a cikin watan Nuwanba na shekarar baɗi kamar yadda aka tsara. A gobe Alhamis aka shirya Ƙungiyar ECOWAS za ta yi wani taro na musammun domin tattauna batun na Burkina Faso.