1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ecowas za ta tattauna batun Nijar

Abdourahamane Hassane
December 10, 2023

Yanzu haka haka dai hankali ya karkata a kan wannan taro na kungiyar ECOWAS da zai gudana a Abuja babban birnin Najeriya a game da shawara da kungiyar za ta yanke a kan Nijar,ko dai cire mata takunkumi ko kuma ci gaba.

Hoto: Xinhua News Agency/picture alliance

 Yau aka shirya shugabannidaga kungiyar raya tattalin Arzikin Kasashen yankin yammacin Afrika wato  ECOWAS za su gudanar da wani taro a Abuja babban birnin Najeriya. Ana sa ran taron zai tattauna batutuwan da suka shafi juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar da yunkurin kwace mulki a Saliyo da Guinea Bissau.Kungiyar ta ECOWAS ta sakawa Nijar takunkunmi karya tattalin arziki bayan da  sojoji suka kifar da gwamnatin fara hula ta  Bazoum Mohmed a cikin watan Yulin da ya gabata.