1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS za ta yi taro kan juyin mulkin sojoji a yankin

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 1, 2023

Ko a ranar Lahadin da ta gabata wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Saliyo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21

Hoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS za su gudanar da wani babban taro a cikin wannan wata na Disamba, don tattauna matsalolin da ke addabar yankin na juyin mulkin sojoji a kasashe irin su Mali da Burkina Faso da Nijar da Guinea, da kuma ayyukan ta'addanci a kasashen Sahel.

Karin bayani:Karar da Jamhuriyra Nijar ta shigar kotun ECOWAS

Wannan na cikin wata sanarwa da ofishin shugaban kasar Cote d'Ivore Alassane Ouattara ya fitar bayan tattaunawa da jagororin kungiyar, yana mai cewa za a gudanar da taron ne ranar 10 ga wannan wata na Disamba a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

A cikin watan Agustan da ya gabata ne dai jagororin kungiyar suka gudanar da taronsu na karshe, inda suka tattauna batun juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, tare da hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.

Karin bayani:Kasar Togo za ta sasanta Nijar da kungiyar Ecowas

Ko a ranar Lahadin da ta gabata wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Saliyo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21.