1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaZambiya

Zambiya: Ko akwai sauran tsohon shugaba a raye?

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 5, 2025

Rahotanni daga Lusaka babban birnin Zambiya na nuni da cewa, tsohon shugaban kasar Edgar Lungu da ya kwashe kusan shekaru bakwai yana mulki ya rasu.

Zambiya | Lusaka | Edgar Lungu | Makoki
Tsohon shugaban kasar Zambiya da ya rasu yana da shekaru 68 Edgar LunguHoto: Philippe Wojazer/Reuters/Pool/picture alliance

Cikin wata sanarwa da jam'iyyarsa ta the Patriotic Front ta fitar, ta nunar da cewa tsohon shugaban na Zambiya Edgar Lungu mai shekaru 68 a duniya ya jima karkashin kulawa ta musamman a wani asibiti da ke birnin Pretoria na Afirka ta Kudu. Wani faifen bidiyo da aka yada ta kafafen sada zumunta ya nuna 'yar Mr.Lungu Tasila Lungu-Mwansa na bayyana cewa, mahaifinta na karkashin kulawar likitoci a makonnin baya-bayan nan.

Edgar Lungu yayin sallama da gawar tsohon shugaban Zambiya Kenneth KaundaHoto: AFP/Getty Images

A shekara ta 2021 ne dai Lungu da ya kasance kwararren soja ya sauka daga kan madafun ikon Zambiya, bayan da babban jagoran adawa kana shugaban kasar na yanzu Hakainde Hichilema ya lashe zabe da dan kankanin rinjaye. Lungu wanda kuma ya sha alwashin sake tsaya wa takara a shekara ta 2026 da ke tafe, ya dare kan madafun iko a shekara ta 2015 bayan da wanda ya gada Michael Sata ya rasu a kan karagar mulki.