1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Editan Canal 3 na Nijar ya shaki iskar 'yanci

January 21, 2025

Gwamnatin Sojin Jamhuriyar Nijar ta saki Seyni Amadou editan gidan talabijin na Canal 3 TV wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar manufofin sojojin kasar tun bayan juyin mulki.

Shagaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Shagaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Hukumomin Nijar sun cafke 'dan jaridar kwana guda da ministan sadarwar kasar Sidi Raliou Mohamed, ya sanar da dakatar da ayyukan gidan talabijin din sakamakon zarginsu da yada farfaganda kan gwamnatin sojin.

Karin bayani: 'Yan jarida na aiki cikin wahala a Afirka 

Shugaban gidan talabijin din Ismael Abdoulaye ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa tuni sojojin suka saki 'dan jaridar Seyni Amadou tare kuma da dawo masa da lasisin gudanar da aikinsa da kuma na kafar yada labaran da yake yi wa aiki wanda sojojin suka dakatar tun da fari.

Karin bayani: RSF ta bukaci Nijar ta sako 'yar jarida da ta kama 

Kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa Reporters Without Borders ta yi tir da cafke 'dan jaridar. Kazalika a rahoton ta na 2024, kungiyar ta RSF ta dora Jamhuriyar Nijar a matsayin kasa ta 80 daga cikin 180 da ke cin zarafin 'yan jarida tare kuma da hana su gudanar da ayyukansu cikin lumana.

A baya bayan nan hukumomin kasar sun dakatar da ayyukan wasu kafafen yada labarai a kasar ciki har da  France 24 da Radiyo RFI da BBC.

     

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW