EFCC a Najeriya ta gurfanar da Sambo Dasuki a kotu
December 14, 2015Talla
Kudaden dai sun hada salwantar dala bilyan 2.1 da aka kebe domin yakar ayyukan kungiyar Boko Haram.
A yayin bayyanar sa a kotun tarayyar kasar a yau Sambo Dasuki gami da tsohon direktan kudin sa Shu'aibu Salisu dukkanin su sun musanta zarge-zargen da ake musu.
Bugu da kari a ta cewar Hukumar EFCC Shu'aibu Salisu ya bayyana karbar dala milyan 47 wadan da suke makare a cikin wasu akwatuna 11 daga babban bankin kasar tare da mika su ga Sambo Dasuki a shekarar da ta gabata.
Tun dai kama madafun ikon Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya dau alwashin yaki da cin hanci da rashawa gami da bankado almundahanar bilyoyin kudade a kasar.