EFCC: Binciken 'yan APC ya tayar da kura
May 4, 2017Na baya-bayan nan dai a cikin binciken na zaman tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwanso da ya samu ziyara ta jami'an 'yan sanda ya zuwa gidan kaninsa garin Madobi da ke jihar Kano da nufin bankado kudade da makamai da ake da tunanin tsohon gwamnan ya boye. Kwankwaso dai na zaman sanatan jam'iyyar APC mai mulki na uku da ya fuskanci ziyara ta jami'an tsaron cikin sabon shiri na bankado kudade da makamai na gwamnatin ta Najeriya.
Tun kafin shi, dama 'yan sandan sun ziyarci gidan tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Danjuma Goje da kuma Sanata Sabo na Kudu daga jihar Jigawa. Wannan abu dai daga dukkan alamu ya harzuka 'yan APC din da suka taka rawa wajen tabbatar da sauyi ga kasar amma kuma ake kallon sauyin na neman wucewa da saninsu. Duk da cewar dai a fadar tsohon gwamnan na Kano 'yan sandan sun kare tare da cin karo da zomaye maimakon akwatunan kudi ko na makamai dai, sabon yanayin da ke zaman manufa ta gwamnatin APC na da bukatar taka tsan-tsan da ma sanin yakamata a fadar kwankwason.
To sai dai kuma ko bayan 'yan APC din dai, su ma 'yan jam'iyyar PDPD da ke adawa a halin yanzu na taraddadi a fadar, mataimakin shugaban majalisar dattawan Tarrayar ta Najeriya Sanata Ike Ekweremadu da ya ce ana shirin a tura makamai da kudade a gidansa, zargin kuma da hukumar EFCC ta ce ya yi kama da mafarkin rana ga duk wanda ya ke takama da gaskiya cikin harkokinsa. To sai dai kuma a fada ta Kwankwason akwai tsoron yi wuwar rikidewar yakin hancin ya zuwa tsohuwar siyasar gaba, wanda a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakaki na gwamnatin sabon yakin ba shi aboki balle makiyi sai dai kowa tasa ta fishe shi.