Ehud Olmert ya shiga tsaka mai wuya
September 4, 2006Kwanaki kaɗan bayan yaƙin da aka gwabza tsakanin Isra´ila da dakarun Hizbullahi , Praminista Ehud Olmert, ya shiga wani hali na tsaka mai wuya.
Bayan zargin da a ka yi masa, na taka mummunar rawa, a cikin yaƙin, yanzu kuma, komitin bin diddiƙin tattalin arzikin ƙasa ya tuhume sa, da hannu cikin wata sabuwar badaƙƙala.
Komitin ya bukaci ya buɗa bincike, na maussaman , domin gano gaskiya a kan zargin da a ka yiwa Ehud Olmert, na naɗa wasu ma ´aikata 4, ba bisa ƙa´ida ba,a lokacin da ya riƙe matsayin ministan kasuwanci da makamashi.
Komitin na kyauttata zaton, Ehud Olmert, ya bi san zuciyar sa, a lokacin da ya naɗa mutanen 4, ta la´akari da cewar, basu dace ba, ko miciƙala zaratin,a wannan wurare.
A ɗaya hannun kuma, idan ba a manta ba, a kwanakin da su ka gabata, an zargi Praminsita Isra´ila da almmudahana da dukiyar ƙasa, a sakamakon gano wani hamshaƙen gida da ya mallaka a birnin Ƙudus.