1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ekweremadu zai shafe shekaru 10 a kurkuku

May 5, 2023

Wata kotu a birnin London ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu hukunci bisa laifin safarar wani matashi da nufin cire kodarsa.

Hoto: Clara Molden/empics/picture alliance

An yanke masa hukuncin daurin shekaru 9 da watanni 8 a gidan yari bisa laifin safarar wani matashi da nufin cire kodarsa domin dasawa 'yarsa da bata da lafiya a wani asibiti a Birtaniya. 

Tsohon dan majalisa mai shekaru 60 da haihuwa da mai dakinsa Beatrice da kuma likitan da ya shiga tsakani dukanninsu sun amsa laifin wanda ya sabawa dokokin Birtaniya na safarar sassan jikin dan adam. 

A cikin makwannin da aka dauka ana gudanar da shari'ar, matashin mai shekaru 21 da aka dauko shi daga jihar Legas din Najeriya, ya tabbatar da cewa an kai shi Birtaniya ne da zumar cire masa koda bisa tukuicin kimanin Euro dubu 8, wanda bai fahimci hakan ba sai bayan da suka isa asibiti a Birtaniya. 

A yanzu haka dai manazarta a Najeriya na ci gaba da tsokaci kan hukuncin da aka yanke wa tsohon dan majalisar, da kuma irin darasin da ya dace 'yan siyasar kasar su koya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani