1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Elbaradei ya kafa sabuwar jam'iyya a Masar

Zainab MohammedApril 28, 2012

Tsohon shugaban hukumar kula da makamashi ta ƙasa da ƙasa, ya ce hakan na da nufin cikanta muradun juyin juya hali

Pro-reform leader and Nobel peace laureate Mohamed El-Baradei, center, wears an Egyptian flag draped on his shoulders as he is surrounded by protesters during his arrival for Friday prayers in Tahrir Square in Cairo, Egypt, Friday, Nov. 25, 2011. Tens of thousands of protesters chanting, "Leave, leave!" are rapidly filling up Cairo's Tahrir Square in what promises to be a massive demonstration to force Egypt's ruling military council to yield power. The Friday rally is dubbed by organizers as "The Last Chance Million-Man Protest," and comes one day after the military offered an apology for the killing of nearly 40 protesters in clashes on side streets near Tahrir over the last week. (Foto:Bela Szandelszky/AP/dapd)
Hoto: dapd

Fitattcen ɗan adawa a Masar Mohammed Elbaradei, ya gabatar da sabuwar jam'iyya a yau, wadda a cewarsa ke da nufin samar da haɗin kai tsakanin al'ummar ƙasar, da cimma manufofin juyin juya hali. Ya fada wa taron daruruwan waɗanda suka halarci kaddamar da jam'iyyar a birnin Alkahira cewar, makomar Masar na fuskantar ruɗani na rashin sanin tabbas a siyasance. Jam'iyyar mai suna tsarin mulki acewar tsohon jagoran hukumar kula da makamashi ta ƙasa da ƙasar, nada akidar tabbatar da ƙasa dake kan tafarkin ingantacciyar democraɗiyya mai adalci da gaskiya. Elberadei yayi fatan sabuwar jam'iyyar tasa, za ta samu magoya baya miliyan biyar, ciki har da ƙwararrun ƙasar ta Masar. Ya ce ko da yake an makara wajen gabatar da jam'iyyar, akwai fatan cewar a ƙarshe zata cimma muradun kafuwarta. Kaddamar da sabuwar jam'iyyar ta Mohammed Elbaradei na zuwa ne wata guda gabannin gudanar da zaben shugaban kasa karon farko, bayan hamɓarar da Hosni Mubarak a watan Febrairun shekarar da ta gabata. A watan Janairu ne dai Elbaradei ya janye daga takarar kujerar shugaban ƙasar, bisa adawarsa da mulkin soji, inda a cewarsa ba za a gudanar da tsabtataccen zaɓe ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu