1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasar Turai: Emmanuel Macron ya zama gwarzo

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
May 10, 2018

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga Jamus da ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen Kungiyar Tarayyar Tura, domin a tafi tare a tsira tare.

Verleihung Internationaler Karlspreis an Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel MacronHoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

Shugaban Faransan Emmanuel Macron ya yi wannan kira ne a birnin Aachen na Jamus, lokacin da yake karbar lambar yabo ta Charlemagne saboda sabbin manufofinsa ga Turai. A hirar da tashar DW da ARD suka yi da shi, shugaban Faransan ya jaddada bukatar kungiyar EU ta yi magana da murya guda, musamman bisa la'akari da cewar Berlin na jan kafa dangane da manufarsa ta sake yin garan bawul ga kungiyar Tarayyar Turan, ta yadda za ta samu ministan kudi guda daya. A dai-dai lokacin da Amirka ta kama hanyarta bayan watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran da yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi da kuma barazanar hukunta abokan kasuwancinta da haraji, Macron ya ce Turai na cikin wani hali na neman mafita, sai dai wajibi ne ta kasance mai hangen nesa. Dan gane da ficewar Amirka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran kuwa, cewa ya yi wannan babban kuskure ne a bangaren Trump:

Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Reuters/W. Rattay

Ya ce "A ganina abu mai muhimmanci shi ne samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. A birnin Washington, D.C. na riga na fada cewar, na fahimci manufar Shugaba Trump na shirin fita daga yarjejeniyar nukiliya da aka cimma a watan Yulin 2015. Dangane da hakane a taron manema labarai na hadin gwiwa da muka yi da shi, na gabatar da manufar aiki akan abubuwa da dama. Na yi nadamar wannan hukuncin da shugaban Amirkan ya yanke, a ganina kuskuke ne. Don haka ne mu ka yanke hukuncin ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar kuma na samu damar fadawa shugaba Rouhani na Iran hakan."

Macron ya gagara hana Trump fita daga yarjejeniyar


A kwanakin baya nedai Macron ya kai ziyara kasar Amirka, ziyarar da ke bangaren kokarin shawo kan Donald Trump da ya ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar, sai dai kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Macron ya lashe kyautar gwarzon Turai

03:10

This browser does not support the video element.

"Ya ce lokacin da na ke birnin Washington, D.C. na yi kokarin nunawa Shugaba Trump cewar kada ya yi watsi da komai, tun da yana shakka game da Iran, bari mu sake karfafa matakai na duban batun, hakan ne zai taimaka wajen cimma manufar da aka sanya gaba. Hakan zai taimaka wajen ganin cewar Iran ba ta koma harkokinta na nukiliya ba. Don haka wajibi ne kasashen Turai mu kasance tsintsiya madaurinki daya, domin aiki da abokan huldarmu wajen ganin cewar lamura basu kazance a wannan yakin ba".

Manazarta na ganin cewar duk fafutukar da shugaba Emmanuel Macron na Faransa ke yi ta kawo sauyi a nahiyar Turai, babu abin da zai tabuka ba tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ba.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani