Yarjejeniyar Kamaru da Equatorial Guinea
March 19, 2023Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ne ya sanar da kulla sabuwar yarjejeniyar da takwaransa na kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema. Shugabannin biyu sun amince da yarjejeniyar ta hako danyen mai da iskar gas a kan iyakokinsu yayin taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka ta CEMAC da ya gudana Juma'ar da ta gaba a birnin Yaoundé na Kamaru.
Wakilin gwamnatin Kamaru Dalvaris Ngoudjou ya ce yarjejeniyar za ta mayar da hankali kan daidaita zuba hannun jari a bangaren iskar gas a tsakanin kasashen biyu. Ya ce a karkashin yarjejeniyar Equatorial Guinea za ta sarrafa gas din Kamaru.
To ko wane irin alfanu Kamaru za ta samu a wannan yarjejeniyar a daidai lokacin da hankulan kasashen yammacin duniya ya karkata kan nahiyar Afirka don neman makamashi saboda yakin Rasha da Ukraine? Masanin tattalin arziki Edmond Kuate a Kamaru ya ce matakin zai kawar da matsalolin da Kamaru ta samu bayan da gobara ta lalata kamfanin sarrafa gas na Sonara.