1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta yi biris da kiran tsagaita wuta

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
October 16, 2019

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi biris da kiran tsagaita luguden wuta a arewacin Siriya, har sai ta kakkabe gungun 'yan ta'adda da suka yi kaka-gida a yankin iyakar kasar Turkiyya da Siriya.

Türkei PK Erdogan Syrien Invasion
Hoto: Presidential Press Office

Shugaban Recep Tayyip Erdogan na kalamun ne a yayin da a ranar Alhamis wasu kusoshin gwamnatin Amirka da suka hada da mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence da sakataren harkokin waje Mike Pompeo, za su gana da shugaban na Turkiyya domin tattauna batun tsagaita luguden wutar da Turkiyya ke yi a arewacin Siriya. 

Kawo yanzu dai manyan kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da matakin na hukumomin Ankara, inda nan a wannan Laraba ake sa ran Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama na musamman kan wannan batu.