SiyasaTurai
Erdogan ya kaddamar da sabon tsarin tsaron sararin samaniya
August 27, 2025
Talla
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kaddamar da garkuwar tsarin tsaron sararin samaniyar kasar da ake yi wa lakabi da "Steel Dome".
Karin bayani:Ba za mu yi watsi da shirin nukiliya ba - Araghshi
Erdogan ya bayyana cewa wannan tsari na tsaron sararin samaniyar kasar ya tabbatar da gawurtar Turkiyya ta fuskar kare kan ta daga duk wata barazana ta tsaro, kamar yadda ya shaida wa dandazon dakarun sojin kasar a barikin kera makamai na Aselsan.
Karin bayani:Turkiyya za ta taimaka wajen bunkasa makamashin iskar gas a kasar Siriya
Shugaban ya kara da cewa gwamnatin Ankara ta kashe sama da dala miliyan $460 wajen samar da motoci masu sulke kimanin 47 domin kare sararin samaniyar kasar daga farmaki.