Erdogan ya nemi a kakaba wa Isra'ila takunkumi kan makamai
October 18, 2024Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kakaba takunkumin hana saye da sayar da makamai a kan Isra'ila don kawo karshen rikicin Zirin Gaza. Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ganawar da ta dauki sa'o'i a Istanbul tsakaninsa da ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Iran da Armeniya da Azarbaijan.
Karin bayani: Tuni da ranar harin ba-zata a Isra'ila
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Hamas ta bayyana cewar ba za ta sako mutanen da take garkuwa da su a Zirin Gaza ba matikar Isra'ila ba ta kawo karshen hare-haren da take kai wa yankin ba, duk kuwa da tabbatar da mutuwar shugabanta Yahya Sinwar da ta yi. Ita dai Hamas da ke iko a Gaza tun 2007 ta ce wannan mutuwar za ta kara karfafa yunkurinta na kwatar 'yancin Falasdinawa, yayin da firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce mutuwar Yahya Sinwar ta zama damba ta kawo karshen yaki a Gaza.
Karin bayani: Me goyon bayan Israila ke nufi ga Amurka?
Wasu shugabannin kasashen duniya sun sabunta kiran tsagaita wuta a Zirin Gaza bayan da Isra'Ila ta kashe shugaban kungiyar Hamas Yahya Sinwar. Shugaban Amurka Joe Biden ya kwatanta kisan Sinwar da kisan Osama bin Laden, inda ya ce wata dama ce ta tunawa da makomar Gaza, ba tare da babakeren Hamas ba.