1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bikin rantsar da Shugaba Erdogan

Ramatu Garba Baba
June 3, 2023

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin karfafa dangantakar diflomasiyya da sauran kasashen duniya a yayin da ya dauki alkawarin inganta tattalin arzikin Turkiyya.

Shugaba Erdogan da matarsa Emine
Shugaba Erdogan da matarsa EmineHoto: Press Office of the Republic of Turkey/AFP

Zababben shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin karfafa dangantakar diflomasiyya da sauran kasashen duniya a yayin da ya dauki alkwarin kara inganta tattalin arzikin kasar, tare da samar da sabbin sauye-sauyen da za su ciyar da kasar gaba.
Erdoghan ya fadi hakan ne bayan shan rantsuwar shugabancin kasar a sabon wa'adin mulki a karo na uku a wannan Asabar a sakamakon nasarar da ya samu a zagaye na biyu na zaben kasar da ya gudana a makon da ya gabata. Shugabannin kasashen duniya akalla 21, da firaminista 13 ne ke halartar bikin shan rantsuwar na Erdogan a birnin Ankara.