1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Kokarin dawo da yarjejeniyar fitar da hatsi

September 4, 2023

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai isa Rasha domin ganawa da shugaba Putin kan batun dawo da yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine ta tekun Bahar al-Aswad.

Erdogan zai gana da Putin kan fitar da hatsin UkraineHoto: Vyacheslv Prokofyev/EPA-EFE

Shugabanni biyu za su tattauna a birnin Sotchi da ke Kudu masu Yammacin Rasha tare da fatan cimma matsaya mai dorewa kan batun fitar da kaya daga Ukraine da kuma duba yiwuwar sasanta Moscowa da Kiev kan yakin da suka share sama da shekara guda da rabi suna gwabzawa.

Karin bayani: Yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine na tangal-tangal

 

Wannan tattaki na mista Erdogan na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta yi barazanar hana Ukraine fitar da hajoji ta teku tare da zafafa hare-haren bama-bamai a tashoshin jiragen ruwan kasar.

Karin bayani: Turkiyya na rarrashin Rasha kan jigilar abincin Ukraine

Rasha dai ta fice daga wannan yarjejeniya ne a watan Julin da ya gabata tana mai sukan matakin hana mata fitar da kayayyaki ciki har da amfanin gona da sinadaren hada takin zamani sakamakon takunkumai da kasashen Yamma suka kakaba mata.