1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

EU ta bukaci a dakatar da tattaunawar nukiliyar Iran

March 11, 2022

A cikin tattaunawar ta Vienna dai an tsara sanya Amirka fara janye wa Iran takunkuman karya tattalin arziki, yayin da ita kuma Iran za ta zabtare amfani da makamashin nukiliya domin a hana ta kera makaman nukiliya. 

UN Sitzung | Josep Borrel und Amir Abdollahian
Hoto: isna

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce akwai bukatar a dakatar da farfado da tattaunawar nukiliyar Iran ta 2015 da take jagoranta. Wannan ya biyo bayan wasu bukatu da Rasha ta sanya a cikin tattaunawar da suka tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin manyan kasashen duniya. 

Babban mai kula da harkokin ketare na Turai Josep Borrel ya rubuta a wannan Jumma'a a shafinsa na Twitter cewa tattaunawar nukiliyar da ke gudana a birnin Vienna ya kamata a dakatar da ita a sakamakon katsalandan da ake samu daga wasu wurare.