1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Babu adalci a gwajin corona ga matafiya daga China

Abdullahi Tanko Bala
December 29, 2022

Hukumar yaki da cutattuka masu yaduwa ta tarayyar Turai ta ce ta yi amanna matakin tilasta yin gwajin Corona ga matafiya da suka fito daga China bai dace ba.

China | Passagiere mit Masken im Flughafen Peking
Hoto: Kyodo/picture alliance

Amirka da wasu kasashe sun sanya dokar tilasta yin gwajin Corona ga matafiya da suka fito daga China.

Sai dai matakin bai zama wajibi a kasashen Turai baki daya ba a cewar hukumar kula da cutattuka masu yaduwa ta tarayyar Turai ECDC

A wannan makon China ta sanar da cewa za ta sassauta dokar kulle ga matafiya da suka shiga kasar na killace kai na wasu yan kwanaki domin tabbatar da cewa basa dauke da kwayar cutar Corona.