EU ta cimma yarjejeniya kan riga-kafin corona
November 10, 2020Talla
Shugabar Hukumar Ursula von der Leyen ta ce hukumar za ta tabbatar da yarjejeniyar a ranar Laraba baya aiki tukuru da ta yi don tabbatar da yiwuwar samun maganin riga-kafin a watannin da suka gabata. Kamfanin hada magungunan na Pfizer dai ya ce sakamakon gwajin farko na riga-kafin na da ingancin da zai yi tasiri ga cutar da kashi 90.
Tuni ma dai hukumar zartaswar ta Tarayyar Turai ta riga ta kulla wasu yarjejeniya tare da kamfanonin hada magunguna da zai bai wa mambobinta 27 damar sayen allurai na yiwuwar riga-kafin coronavirus kimanin biliyan daya.