Kasashen Sahel uku ne ke fuskantar karancin cimaka
October 20, 2020A wani taron da kasashen Jamus da Denmark suka jagoranta, karkashin kungiyar Tarayyar Turai gami da Majalissar Dinkin Duniya, ya sanar bayar da tallafin Euro miliyan43 ga kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso domin tsamosu daga fadawa cikin kangin karancin cimaka.
Mai magana da yawun kungiyar ta Tarayyar Turai Balazs Ujvari ya ce an ware Euro miliyan 23 domin gudanar da ayyukan jin kai a kasashen, inda kuma za a yi amfani da Euro miliyan 20 wajen yaki da yunwa.
A wajen taron an bayyana kasashen uku a matsayin wadanda suka fi ko wace kasa a yankin Sahel fuskantar barazanar afkwa cikin karancin cimaka, sakamakon sauyin yanayi da karuwar al'umma.
Yara da dama ne dai taron ya ce basu samun damar zuwa makaranta. Wasu alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa mutane sama da miliyan 13 ne ke bukatar agajin gaggawa a iyakokin kasashen guda uku.