EU za ta tallafa wa kasar Lebanon
August 7, 2020Talla
Kungiyar EU ta ce ta na goyon bayan taron gidauniyar tattara kudade don tallafi ga jama'ar da iftila'in fashewar wasu ababe ya shafa a da ya hallaka akalla mutane 150, wasu kimanin 5000 kuma suka ji rauni.
Tuni shugaban hukumar zartawar kungiyar ta EU Charles Michel ya bayyana anniyarsa ta kai ziyarar aiki a birnin Beyrouth a ranar Asabar, domin nuna alhinin daukacin tarayyar Turai ga al'ummar Lebanon, inda zai gana da shugaba Michel Aoun da wasu kusoshin gwamnatin kasar.
Tuni EU ta ware Euro miliyan 33 a matsayin zangon farko na agajin gagawa ga kasar, tare da saka baki ga sauran kasashen nahiyar don kawo nasu dauki ciki gagawa.