1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU: Hasashen ci gaba a kasashe masu amfani da kudin euro

Abdullahi Tanko Bala
November 15, 2024

Hukumar tarayyar Turai ta yi hasashen samun ci gaba da kashi 1.3 cikin dari a kasashen da ke amfani da kudin bai daya na Euro a 2025 yayin da ake fatan samun saukin hauhawar farashin kayayyaki.

Hoto: picture-alliance/dpa/D. Kalker

Tattalin arzikin Jamus wanda shi ne mafi karfi a nahiyar turai, ana sa ran zai ci gaba da yin tangal tangal.

Sai dai kuma hukumar gudanarwar tarayyar Turai ta yi nuni da hadarin da ka iya tasowa daga siyasar kasa da kasa na raunin zuba hannun jari da kuma tsadar rayuwa.