1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta saka wa Iran sabbin takunkumai

Binta Aliyu Zurmi
January 23, 2023

A gaba a wannan Litinin din ministocin harkokin kasashen ketare na kungiyar tarayyar Turai a hukumance za su rattaba hannu a kan sabbin takunkumai da suka laftawa wasu jami'an kasar Iran.

Flagge Iran und EU
Hoto: Zoonar/picture alliance

Jami'an diflomasiyyar EU sun ce kusan mutum 40 da kamfanoni da kungiyoyi ne wannan sabbin takunkuman za su shafa bisa take hakkinn al'umma da suka ce ana yi a kasar ta Iran.

Tun a watan Satumba bayan zanga-zangar da ta barke a kan mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami'an gyara hali na Hisba, Tehran ke amfani da karfi ta na murkushe masu boren. A baya-bayan nan ma ta rataye sama da masu boren 4.

Ko baya ga wadannan takunkuman, ministocin na tafka muhawarar ayyana jami'an hisba Iran a matsayin 'yan ta'adda.