1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Kokarin warware rikicin Ukraine

Riegert, Bernd/ Usman Shehu UsmanFebruary 10, 2015

Jami'an EU na daukar kwararan matakai, domin tabbatar da taron kolin da zai hada da Rasha, Ukraine da shugabanin EU masu shiga tsakani, bai kasance aikin kawai ba.

Merkel bei Obama 09.02.2015
Hoto: picture-alliance/dpa

Tuni kungiyar Eu ta fidda sunayen mutanen da za'a dorawa takunkumin wadanda ake ganin suna da hannu a rikicin gabashin Ukraine.

Babbar matsalar da shiga tsakani a rikicin Ukraine yake fuskanta shi ne, koda su kansu kasashen kungiyar Tarayyar Turai, kansu a rabe yake kan yadda za tinkari rikicin, yayinda wasu kasashen ke neman a tura sojoji, ko kuma akalla makaman yaki don taimkawa sojan Ukraine, amma wasu kasashen na cewa sam, batun makamai din kansa ba mafita bace. Ministan harkokin wajen kasar Lintoniya Linas Linkevicius bayan taron ministocin harkokin wajen EU ya bayyana cewa.

"Dukkanmu muna fatan a samu masalaha a siyasance, babu wanda ke son yaki. To amma za mu yanke hukunci ne bisa abinda ke zahiri a fagen daga. Ba zamu yarda da ko kalma guda dake fitowa a kasar Rasha ba, kalamansu basu da amfani, in bamu gani a kasa ba"

To sai dai manyan kasashen EU kamar Jamus, Italiya, da Ostiriya, suna ganin kara aza takunkumi kan Rasha ba ma futa ba ce.

Hoto: AFP/Getty Images/I. Znotins

Amma a yayin da kasashen Turai ke da rarrabuwar kuwuna kan agazawa Ukaraine da makamai yakin da ta ke yi da 'yan aware, ita kam kasar Amirka tuni ta fara duba wannan zaben, kamar yadda shugaban kasar Amirka Barack Obama ya bayyana yayin ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ziyarar da ta kai kasar Amirka.

"Abinda zan yi shi ne, na bukaci jami'aina su duba duk hanyar da ake iya bi, don kawo sauyi a rikicin, kuma batun turawa Ukraine makaman kare kai na daga cikin batutuwan da muke dubawa"

Martanin bayan kalaman Obama, gwamnatin Rasha ta fidda sanarwar cewa yunkurin Amirka na tura makamai a Ukaraine, ba komai bane illah tinkarar yaki, kuma Amirka na neman kusantar Rasha ta yadda za ta iya kawo sauyin gwamnati a Mosko.