1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Martanin EU kan ajiye takarar Joe Biden

Suleiman Babayo LMJ
July 22, 2024

Ana ci gaba da mayar da martani kan matakin Shugaba Joe Biden na Amurka, na ajiye takarar sake neman shugabancin kasar sakamakon matsin lamba daga jam'iyyarsa ta Democrats.

Amurka | EU | Tuta | Alaka
Akwai kyakkyawar alaka tsakanin kungiyar Tarayyar Turai EU da AmurkaHoto: picture-alliance/dpa/J. Kalaene

Jam'iyyarsa ta Democrats ta bukaci Shugaba Joe Biden na Amurkan ya ajiye kudirin nasa na sake tsayaw takarar shugabancin kasar ne, saboda tsufa da kuma fara rudewa. Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar Tarayyar Turai suna cikin masu mayar da martani kan matakin na Shugaba Biden, inda suka bayyana ra'ayoyinsu kan matakin a taronsu na  wannan Litinin din a kasar Beljiyam.

Karin Bayani: Shugaba Joe Biden ya janye daga takara

A cewar minstar harkokin wajen kasar Beljiyam Hadja Lahbib da ke zaman mai masaukin baki, janyewar Shugaba Biden din daga takara a zaben Amurka bai nuna nasara kai tsaye ga Donald Trump ba. A daya bangaren Hukumar Tarayyar Turai ta ce Amurkawa ne ke da alhakin zaben mutumin da zai jagoranci kasar gami da aiki da sauran shugabannin kasashen duniya, kamar yadda shugaban Hukumar Gudanarwar kungiyar ta EU Josep Borrell ya nunar.

Shugaba Joe Biden na Amurka, lokacin da yake shan rantsuwar kama aiki a 2021Hoto: picture alliance / Consolidated News Photos

Galibin kasashen na Turai sun yi nuni da cewa babu wata damuwa kan wanda ya lashe zaben na Amurka, ganin ko a baya lokacin mulkin tsohon Shugaba Donald Trump ya karfafa matakan tsaron Turan duk da dari-dari da aka nuna game da shi idan ya sake karbe madafun ikon kasar mafi karfin tattalin arzikin tsakanin kasashen duniya. Jamus ta kasance kasa mafi karfin tattalin arziki tsakanin kasashe kungiyar Tarayyar Turan, kuma ministar harkokin wajen kasar Annalena Baerbock ta jinjinawa Shugaba Joe Biden na Amurka kan matakin janye kudirinsa na sake yin takarar shugabancin kasar. A cewarta ya fifita muradun kasarsa, fiye da nasa na kashin kai.

Karin Bayani: FBI ta tabbatar da yunkurin halaka Trump

Bangarori da dama da gwamnatoci na duniya, za su duba yadda abubuwa za su sauya musu ganin tilas a samu sauyi game da shugabancin Amurka duk wanda ya samu nasara a zaben da ke tsafe. Amurka ce dai kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya wadda kuma take da matukar tasiri, inda kasar Chaina ta ce duk abin da ya faru wannan lamari ne na cikin gidan Amurka. Irin wadannan kalaman mai magana da yawun fadar mulkin kasar Rasha Dmitry Peskov ya bayyana, inda yake cewa wanda zai zama shugaban Amurka zabi ne na Amurkawa.