EU na kokarin sake karfafa alaka da Siriya
May 11, 2026
Talla
A wannan Litinin din ce ake sa ran ministocin harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai, EU za su gana da takwaransu na Siriya, Asaad al-Shaibani a birnin Brussels domin fara tattaunawa a hukumance. EU ta ce Siriya na fuskantar matsaloli da dama, inda miliyoyin mutane a kasar ke bukatar abinci da agajin jin kai, yayin da sassan kasar da dama sun lalace sakamakon yakin basasa.
Karin bayani: EU ta dage wa Siriya jerin takunkumai
Tuni dai EU ta yi alkawarin bayar da tallafin euro miliyan 620a tsakanin shekarar 2026 zuwa 2027. A yanzu EU na son ganin Siriyar ta samun zaman lafiya domin ta mayar da 'yan kasar da suka gujewa yaki, gida. Dangantaka tsakanin EU da Siriya ta yi tsami ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar, Bashar al-Assad.