1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin kungiyar EU na neman mafita

Abdul-raheem Hassan
July 2, 2019

Kasashen kungiyar Tarayyar Turai za su sake zama karo na uku a birnin Brussels na kasar Beljiyam domin samar da matsaya kan shugabancin kungiyar.

Bildkombo Mögliche Kandidtaen für die EU-Kommissionspräsidentschaft

Duk da kai ruwa rana kan rashin fahimtar juna tsakanin jiga-jigan kungiyar tsawon kwanaki ana gudanar da taro, amma Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana fatan cimma matsaya tare da nada kusoshin kungiyar a zaman da shugabannin kungiyar za su yi karo na uku.

Ana adai ganin jinkirin samar da sabbin shugubannin kungiyar cikin lokaci ka iya zama matsala da zai rage tasiri da kimar kungiyar da ma tsarin makomarta nan gaba.