1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na niyar ladabtar da Rasha kan Navalny

Mouhamadou Awal Balarabe
September 17, 2020

Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci a kakaba wa Rasha takunkumi bayan da aka zargeta da sanya wa Alexei Navalny guba a lokacin da yakin neman zabe. Sai dai Rasha ta yi tir da wannan mataki.

Außerordentliche Plenarsitzung des EU-Parlaments in Brüssel
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Majalisar dokoki ta Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci a kakaba wa Rasha takunkumi mai tsauri sakamakon sanya wa Alexei Navalny guba da ta yi da nufin murkushe dan adawan. Kudurin da majalisar ta amince da shi a birnin Bruxelles ya yi kira ga Tarayyar Turai da ta tsara jerin matakan takura wa Rasha tare da karfafa takunkumin da aka sanya mata bayan da ta mamaye yankin Kirimiya.

Tuni dai Moscow ta gargadi EU game da takunkumin, inda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha Maria Zakharova ta ce "Duk wani yunkuri na sanya takunkumi da sunan Navalny wani mataki ne na fito na fito da Rasha."


Shi dai Navalny ya fadi ne a watan da ya gabata yayin da yake yakin neman zabe don marawa ‘yan takarar adawa baya a zabe yankuna. Amma a  yanzu haka yana jinya a Jamus, inda masana suka tabbatar da cewa an sanya masa guba ne a ruwan sha na kwalba.