1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai na tattaunawa da Taliban a Brussels

Abdul-raheem Hassan
June 23, 2026

Tarayyar Turai ta karbi bakwancin jami'an Taliban a Brussels don tattauna batun mayar da 'yan Afghanistan da ba su samu mafaka a kasashen Turai ba.

Mullah Baradar Akhund, babban jami'in gwamnatin Taliban. An dauki hoton a wani bidiyo da ba a san inda aka nade shi ba a 2021
Mullah Baradar Akhund, babban jami'in gwamnatin Taliban. An dauki hoton a wani bidiyo da ba a san inda aka nade shi ba a 2021Hoto: SOCIAL MEDIA/REUTERS

Gwamnatin Belgium ta bai wa jami'an Taliban bizar wucin gadi domin halartar taron. Matakin na daya daga cikin manyan matakan inganta hulda tsakanin kungiyar EU da gwamnatin Taliban tun bayan da kungiyar ta karbi mulki a Afghanistan a shekarar 2021.

Tattaunawar na mayar da hankali ne kan batutuwan kaura da yadda za a mayar da wadanda ba su cancanci ci gaba da zama a Turai ba, lamarin da ke ci gaba da haifar da muhawara kan dangantaka da gwamnatin Taliban da kuma kare hakkin dan Adam a kasar Afghanistan.

Gwamnatocin kasashen Turai na kara matsa kaimi wajen daukar tsauraran matakai kan bakin haure, yayin da batun ke ci gaba da daukar hankali ta fuskar siyasa a fadin nahiyar.

Alkaluma daga hukumomin EU, kasashe membobin kungiyar sun karbi kusan bukatun neman mafakar 'yan Afganistan miliyan daya tsakanin 2013 zuwa 2024, an kuma amince da kusan rabin adadin mutanen.

Kimanin kasashen EU 20 ne suka nuna sha'awar mayar da wasu 'yan kasar Afganistan wadanda ba su samu izinin zama ba, musamman wadanda aka samu da aikata manyan laifuka ko kuma wadanda aka yi la'akari da barazanar tsaro a tattare da su.