1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU: Nazarin hulda da sabuwar gwamnatin Trump

Mouhamadou Awal Balarabe
January 22, 2025

Kwanaki biyu bayan rantsar da sabon shugaba Donald Trump na Amurka, majalisar dokokin Tarayyar Turai na tattaunawa kan tasirin da salon mulkinsa zai yi a fannin siyasa da tattalin arziki.

Taron shugabanin kasashen kungiyar tarayyar Turai a Brussel
Taron shugabanin kasashen kungiyar tarayyar Turai a BrusselHoto: SIERAKOWSKI FREDERIC/European Union

A ranar da aka rantsar da Donald Trump, bai dauki wani mummunan mataki a kan Kungiyar Tarayyar Turai ba. Hasali ma dai, har ya zuwa yanzu, sabon shugaban Amurka bai sanar da karin harajin shigo da kayayyaki daga kasashen EU ba alhali a lokacin yakin neman zabe, Trump ya yi barazanar sanya sabon kudin fito da zai kai kashi 10 zuwa 20 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Turai. Saboda haka ne 'yan majalisar dokoki EU ke ganin cewar kungiyarsu ba ta tsone wa Trump ido a sa'o'i na farko na wa'adin mulkinsa na biyu ba. Sai dai, an samu karin tattaunawa tsakanin jiga-jigan EU game da yadda za a tinkari sabuwar gwamnatin Trump.

Karin Bayani: Trump ya yi barazanar kara haraji kan EU

Shugabannin kasashen Turai a BrusselsHoto: John Thys/AFP/Getty Images

A taron tattalin arzikin duniya da aka yi a Davos, shugabar Hukumar Zartaswa ta Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce za su sha yadda Trump ya dama, amma bisa sharadin tsayawa kan ka'idojin EU. Babban abin da Kungiyar Tarayyar Turai ta sa gaba a yanzu, shi ne tattaunawa kan muradan bai daya tsakanin Amurka da EU da kuma bude kofa ga shawarwari. Dama Trump ya ce yana son daidaita gibin kasuwanci da kungiyar EU ta hanyar karin haraji ko kuma ta hanyar fitar da makamashi mai yawa, kamar mai da iskar gas.

A cikin zauren majalisar dokokin Turai, Kwamishinan Kasuwanci Maros Sefcovic ya jaddada cewa EU ta kasance a sahun gaba na masu shigo da iskar gas daga Amurka, inda kusan kashi 50 na nau'in gas na LNG ke fitowa daga Amurka.

Karin Bayani: Turai: Trump ya tayar da zaune tsaye

Tutar Amurka da ta EUHoto: Getty Images/T. Charlier

Sai dai duk da haka, Sefcovic wanda dan asalin Slovakiya ne ya ce a shirye suke su fadada wannan dangantakar hadin gwiwa da sabuwar gwamnatin Trump.  A daya hannun kuwa, ya ce a shirye manyan jami'an EU suke su kare muradunsu. Wannan hanya dai ta yi daidai da abin da Bernd Lange, shugaban kwamitin ciniki, ya kira "harbin tsuntsaye biyu da dutse daya".

Bakunan 'yan majalisar EU sun hadu kan neman hanyar kauce wa rikicin kasuwanci da Donald Trump. Dan majalisa mai wakiltar kasar Spain Francisco José Millan Mon ya bayyana cewar irin wannan yakin kasuwanci ba zai amfani kowa ba. Maimakon haka, dole ne EU ta yi kokarin kulla dangantakar kasuwanci da Amurka. Wannan yana nufin rashin ba da kai domin bori ya hau a kan batun daidaita manyan kamfanonin fasaha ko na sada zumunta na zamani.

Karin Bayani:Turai ta goyi bayan WHO, ta sabawa Trump

Wasu daga cikin shugabannin tarayyar TuraiHoto: SIERAKOWSKI FREDERIC/Europäische Union

Sannan majalisar dokokin Turai ta yi tsokaci a kan yankin Greonland da Donald Trump ke neman mamayewa, inda mai wakiltar Denmark Stine Bosse ya jaddada cewa makomar Greonland za ta kasance a hannun su 'yan yankin ne kawai. Sai dai ko bayan da ya hau kan karagar mulki, Shugaba Trump ya sake nanata cewa Amurka na bukatar Greonland don "tsaro na kasa da kasa." Shi kuwa dan jam'iyyar Social Democrat mai suna Vytenis Povilas Andriukaitis ya soki matakin da Trump ya dauka na dakatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, inda ya ce " abin kunya ne."

Amma yabo ga ayyukan farko na Donald Trump a ofis ya fito ne daga 'yar jam'iyyar AfD mai kyamar baki a Jamus, Christine Anderson, wacce ta ce matakin da shugaban ya dauka na rufe kan iyaka da korar duk bakin haure zai inganta tsaron cikin gida a Amurka.