1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Rage dogaro kan kamfanonin da ba na Turai ba

November 18, 2025

Kasashen Turai sun kudiri aniyar rage dogaro da kamfanonin fasaha wadanda ba na Turai ba

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban gwamanatin Jamus Friedrich Merz da shugaban Faransa Emmanuel Macron da ministocin kungiyar tarayyar Turai EU da shugabannin 'yan kasuwa sun gudanar da taro a birnin Berlin da manufar tattauna hanyoyin da Turai za ta rage dogaro ga kamafanonin fasaha wadanda bana Turai ba.

Taron na fasaha da kasashen Turai suka ya sami halartar daruruwan mahalarta daga kasashe 23 da wakilan 'yan siyasa, da 'yan kasuwa da sauran al'aumma

Minisatan Fasahar zamani na kasar Jamus Karsten Wildberge wanda ya bude taron ya yi kira ga kasashen Turai da su kara hada kai su tunkari kalubale domin su kara zama gagarabadau kuma masu 'yanci daga kamfanonin fasaha da ba na Turai ba.