1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

EU za ta soma amfani da wani sabon nau'in maganin Corona

Abdoulaye Mamane Amadou
December 16, 2021

Hukumar Turai mai kula da magunguna EMA ta amince da a soma amfani da wani sabon nau'in maganin Covid-19 idan bukatar hakan ta taso ga wadanda suka kamu da cutar.

Coronavirus | Pfizer Covid Pille
Hoto: Pfizer/REUTERS

A cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Alhamis, hukumar ta ce duk da yake har yanzu ba a kai ga mika cikakkiyar amincewa da soma amfani da maganin ba, likitoci ka iya amfani da shi idan rashin lafiyar ta tsananta wajen yi wa wadanda suka kamu da cutar magani, madamar marasa lafiyar ba su nuna wata bukata ta naurar da ke taya jama'a numfashi ta oxygène ba.

Kamfanin harhada magungunan nan na Pfizer na daga cikin wadanda suka samar da sabon nau'in maganin, a yayin da duniya ke cikin rudani na sabon nau'in annobar corona ta omicron.