EU: Sabon shirin tsaron nahiyar Turai
October 23, 2025
Shirin da ake fatan kammala shi nan da shekaru biyar masu zuwa ya biyo bayan karin damuwar da ake da ita ne cewa Rasha na bin diddigin lamuran tsaro a kasashe 27 na tarayyar Turai.
Yakin fin karfi da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine da kuma tasirinsa a kan tsaron nahiyar Turai da duniya baki daya ya sanya kalubale ga dorewar rayuwa kamar yadda shugabannin suka baiyana a sanarwar da suka fitar a taron kolin da suka gudanar a Brussels.
Sun yi kira ga gwamnatoci su kara azama kan muhimman ayyukan da za su kaddamar a farkon rabin shekarar 2026 domin dacewa da sabon shirin da suka yi wa lakabi zama cikin shiri a 2030, shirin da hukumar tarayyar Turai ta tsara.
Hukumar tarayyar Turan ta yi kiyasin kudin da za ta kashe kan tsaro a bana zai kai kusan euro biliyan 392 kwatankwacin Dala biliyan 457 wanda ya kusan ninka abin da ta kashe shekaru hudu da suka wuce kafin Rasha ta kai hari kan Ukraine.