EU: Sake gina Ukraine da kudaden Rasha
February 3, 2023Shugaban majalisar Tarayyar Turai Charles Michel da shugabar hukumar tarrayar Turai Ursula von der Leyen ne suka sanar da wannan mataki a cikin sanarwar da suka fitar yayin taron kolin da suka gudanar a wannan Jumma'ar a birnin Kiev kuma Ukraine ta yi marhabin da matakin mai wuyar aiwatarwa duba da wasu tanade-tanaden dokoki.
Ko baya ga wannan mataki, kungiyar tarayyar Turan na son a kafa wani ofishi a kotun hukunta manyan laifuka wanda zai tattara bayanai kan mamayar da Rasha ta kaddamar kan Ukraine kusan shekara guda domin a hukuta kasar kan lafukan yaki.
To sai dai masana harkokin shari'a na ganin da akwai wuya bukatar Turan ta biya domin kafa kotu ta musanman wacce za ta yi irin wannan aiki abu ne mai matukar sakarkakiya domin Rasha da Ukraine ba sa daga cikin kasashen da suka rattaba hannu a kan dokar da ta ba da damar yin hakan.