EU: Shirin sake farfado da tattalin arziki
July 18, 2020Talla
A wani zaman da aka kwashe sa'o'i 14 ana musayar yawu, taron ya sauya fasalin lamura tsakanin ba da rance da kuma tallafi, batutuwan da dama ake da bambancin ra'aya a kansu.
Shawarar Mr. Michel dai ita ce daga cikin euro biliyan 750 din da za a yi amfani da su, euro biliyan 450 za su kasance tallafi, yayin da ragowar 350 kuwa za su kasance kudade na rance.
A baya ya bayar da shawari ne na yin amfani da euro biliyan 500 a matsayin tallafi, sai kuma euro biliyan 250 a matsayin rance.
Wannan sabon tsarin dai ba zai yi wa kasashen Denmark da Sweden da Holland da kuma Austria dadi ba, saboda bukatarsu ta a bayar da kudaden a matsayin rance ba tallafi ba.