EU ta amince da yarjejeniyar CETA
February 15, 2017![Frankreich Demo gegen CETA vor dem Europaparlament in Straßburg](https://static.dw.com/image/37557369_800.webp)
Talla
Shirin da ake kira da suna CETA wanda ya janyo zanga zangar jama'a a birnin Strasbourg na Faransa cibiyar majalisar dokokin ta tarrayar Turai gabannin kada kuri'a 'yan majalisar a kai, ya tanadi soke kudaden fito tsakanin kasashen na Turai da Kanada da kishi 99 cikin dari da kuma hulda a fanin kare muhalli da kiwon lafiya.Masu yin adawa da shirin na CETA na cewar zai janyo koma baya ga manoma a nahiyar ta Turai.