1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yankin Hong Kong na bukatar 'yanci cin gashin kai

Binta Aliyu Zurmi
May 26, 2020

Shugaban majalisar Turai Charles Michel ya bayyan aniyar kasashen nahiyar, na taimaka wa yankin Hong Kong don ganin ya sami 'yancin cin gashin kai.

Belgien | Pressekonferenz Ursula von der Leyen und Charles Michel nach Treffen mit Erdogan
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Michel ya ce EU na kallon duk take-taken da China ke yi musamman ma wadanda suka shafi dangantakarta da wasu kasashen duniya. 

Ya jaddada bukatar sakar wa yankin na Hong Kong mara a lokacin da suka yi wata tattaunawa ta bidiyo da Firaiministan kasar Japan, Shinzo Abe.

Ko baya ga kasashen Turai, su ma mazauna yankin na Hong Kong da masu rajin kare dimokradiyya na ci gaba da martani kan sabbin dokokin da suka danganci tsaro da China ta bijiro da su.

To sai dai yayin da ake ci gaba tsokaci kan lamarin, China ta ce tana kan bakanta na amfani da sabon tsarin tare da gargadin kasashen duniya kan su guji tsoma mata baki a harkokinta na cikin gida.