1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta ja hankalin Amurka kan hana Falasdinawa shiga

August 31, 2025

Tarayyar Turai ta damu da matakin Amurka na hana wasu jami'an falasdinawa shiga kasar saboda halartar taron duniya da za a yi a birnin New York nan gaba kadan.

Kaja Kallas a lokacin taron manyan EU da aka yi a Denmark
Kaja Kallas a lokacin taron manyan EU da aka yi a DenmarkHoto: Thomas Traasdahl/Ritzau Scanpix Denmark/REUTERS

Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci Amurka da ta sake duba shawarar da ta yanke na hana ba da takardun izinin shiga kasar ga jami'an Falasdinu da ke shirin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya na watan gobe, in ji babbar jami'ar diflomasiyyar kungiyar Kaja Kallas.

Kaja Kallas ta yi amfani da dokar kasa da kasa wajen kiran Amurka da ta sauya wannan matakin na musamman, wanda ke kara daidaita gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amurka da gwamnatin Isra'ila yayin da take yaki a Gaza.

Wannan matakin na Amurka ya zo ne a lokacin da Faransa ke jagorantar yunkuri na amincewa da kasar Falasdinu a taron shugabannin duniya da za a yi a New York.

Ministoci da dama a taron birnin Copenhagen na kasar Denmark, sun jaddada kiran Faransa na bukatar Amurka ta ba da damar shiga ga tawagar Falasdinu.