EU: Allurar rigakafi don yaki da mura
July 15, 2020Talla
Hukumar tarayyar Turan na fatan kawar da yiwuwar sake cushewar asibitoci da marasa lafiya kamar yadda aka gani lokacin kololuwar yaduwar annobar corona a nahiyar Turai a tsakanin watan Maris da Aprilu.
Mataimakin shugaban hukumar tarayyar Turan Margaritis Schinas, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen turan su sayi karin magungunan mura su kuma tabbatar da cewa an yiwa mutane da dama allurar rigakafin.
Hedikwatar tarayyar Turan a Brussel na son ganin gwamnatoci sun yi amfani da manhajar gano mutane da ke dauke da cutar corona, sai dai kawo yanzu kasashe goma ne kacal daga cikin kasashe 27 na tarayyar Turan suke amfani da manhajar.