1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yi tir da matakin rufe ofishin DW a Moacow

Binta Aliyu Zurmi
February 4, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da matakin da mahukuntan Rasha su ka dauka na rufe ofishin tashar Deutsche Welle da ke birnin Moscow.

Peter Stano I  Sprecher der Europäischen Kommission für Außen- und Sicherheitspolitik
Hoto: Dursun Aydemir/AA/picture alliance

Da yake jawabi ga manema labaru, mai magana da yawun Kungiyar ta EU a kan harkokin kasashen ketare, Peter Stano ya ce wannan mataki ne da ba za su amince da shi ba, ya kuma ce Rasha ta nuna yadda ta ke ci gaba da murkushe 'yancin yada ayyukan jarida.

Wannan matakin da Rasha ta dauka dai na zuwa ne bayan da Jamus ta haramta watsa wasun shirye-shirye cikin harshen Jamusanci a tashar Russia Today wanda kuma Stano ya ce ko kusa ba su da alaka da abin da Rashar ta yi.

EU ta ce tana goyon bayan tasahar DW da ma ma'aikatan da abin ya shafa. Wannan sabuwar ta'akadamar ta kara rura wutar rikici da dama can ke ci tsakanin mahukuntan na Moscow da EU a game da yunkurin mamaye wani yanki na Ukraine.