SiyasaTurai
EU ta cimma matsaya kan 'yan gudun hijira
October 4, 2023![Ceton 'yan gudun hijira a kan teku](https://static.dw.com/image/66955566_800.webp)
Talla
Kasashen na EU dai sun bukaci sabunta manufofin ne yadda za su tunkari matsalar 'yan gudun hijirar idan aka sami kwarar masu neman mafaka zuwa cikin tarayyar Turai.
A wannan makon shugabannin kasashen Turan za su hallara a birnin Granada da ke kudancin kasar Spain domin tattauna batun bakin hauren.
Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta jinjinawa yarjejeniyar da za ta sauya lamura.